A yau Laraba, mai magana da yawun babban yankin kasar Sin ya bayyana cewa za a yi la’akari sosai da asalin hakikanin abubuwan da ke tsibirin Taiwan yayin aiwatar da manufar “kasa daya mai tsarin mulki biyu” a yankin, kana za a himmatu sosai wajen aiwatar da manufar domin warware batun Taiwan.
Da yake jawabi ga taron manema labarai, mai magana da yawun ofishin kula da gudanar da al’amuran yankin Taiwan na majalisar gudanarwar kasar Sin Chen Binhua, ya bayyana cewa, babban yankin na Sin zai ci gaba da hada kai da masu nuna kishi da ‘yan uwantaka na yankin Taiwan tare da yin nazari sosai ga samar da mafita ga Taiwan, domin kara himmar sake hadewa cikin kwanciyar hankali.
Ya kara da cewa, za a yi cikakken la’akari da hakikanin gaskiyar abubuwan da ke yankin Taiwan, da ra’ayoyi da shawarwarin al’umma daga kowane sashe na rayuwa na bangarorin tsibirin Taiwan da kuma duba muradun mutanen yankin. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp