Firaminsitan kasar Sin Li Qiang, ya lashi takobin kasarsa za ta fadada bude kofarta tare da mayar da babbar kasuwarta zuwa mai samar da dimbin damarmaki ga duniya.
Li Qiang ya bayyana haka ne a jawabin da ya gabatar yayin bikin bude baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin (CIIE) karo na 7, da kuma taron dandalin tattauna harkokin tattalin arziki na kasa da kasa na Hongqiao, a birnin Shanghai.
- Xi Ya Taya Boko Murnar Zabarsa A Matsayin Shugaban Botswana
- An Bude Baje Kolin CIIE Karo Na 7 A Birnin Shanghai
A cewarsa, shirya bikin na CIIE wani muhimmin mataki da Sin ta dauka na fadada bude kofa da hadin gwiwa, wanda ke bayyana kyakkyawan kudurinta ga duniya.
Firaministan ya kuma jaddada bukatar karfafa cimma matsaya daya kan bude kofa, yana cewa, ya kamata dukkan bangarori su hada hannu su nace ga ka’idoji da tsare-tsaren cinikayya da tattalin arziki na duniya, kana su cika tanade-tanaden yarjejeniyoyin tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin kasa da kasa da bangarori da dama.
Bugu da kari, ya ce Sin za ta fadada bude kofarta zuwa babban matsayi, ta yadda zai dace da mizanin ka’idojin cinikayya da na tattalin arziki na duniya, yana mai alkawarin za a yi kokarin aiwatar da dabarun daukaka yankunan gwajin cinikayya mara shinge. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)