Wasu rahotanni na cewa dakarun RSF a kasar Sudan, sun hallaka fararen hula kusan 2000 a birnin El Fasher, fadar mulkin jihar arewacin Darfur. Kuma tuni MDD, da kungiyar tarayyar kasashen larabawa ta AL, da kungiyar tarayyar Afirka ta AU, da ma wasu karin hukumomin kasa da kasa suka fara mayar da hankali kan yanayin jin kai da ake ciki a birnin na El Fasher, suna masu Allah wadai da muggan ayyukan da ake aikatawa kan fararen hula.
Game da hakan, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta bayyana a Litinin din nan, yayin taron manema labarai cewa, Sin na Allah wadai da duk wasu ayyuka dake illata fararen hula, tana kuma fatan Sudan za ta cimma nasarar tsagaita bude wuta da gaggauta kawo karshen yaki. (Saminu Alhassan)
			




							








