A yau Juma’a ne mazauna birnin Nanjing suka yi bikin tunawa da mutanen birnin da aka hallaka kimamin 300,000, yayin kisan kiyashin da ya auku a lokacin yakin duniya na 2. Kaza lika, gwamnatin kasar Sin ta yi bikin makokin mamatan.
Tun da karfe 8 na safiyar Juma’ar nan ne aka sauko da tutar kasar Sin zuwa rabin sanda, a babban dakin tunawa da mamatan da dakarun kasar Japan suka hallaka a birnin Nanjing.
- Xi Ya Gabatar Da Muhimmin Jawabi A Babban Taron Ayyukan Tattalin Arziki Na Tsakiya
- Birnin Yiwu Na Kasar Sin Zai Kaddamar Da Sabon Zagaye Na Gyare-gyaren Cinikayyar Duniya
Da misalin karfe 10 da minti 1 na safiya kuma aka kunna jiniya. A lokaci guda direbobin motoci dake zirga zirga a kan tituna suka dakata, tare da dannan hon din motocinsu, yayin da su ma masu tafiya a kafa suka tsaya na dan lokaci domin jimami da tunawa da mamatan.
Memba a ofishin hukumar siyasa ta kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban hukumar watsa bayanai ta kwamitin kolin jam’iyyar, Li Shulei, ya halarci bikin tare da gabatar da jawabi. (Saminu Alhassan)