Zaunannen wakilin kasar Sin dake ofishin MDD a Geneva da sauran kungiyoyin kasa da kasa Chen Xu ya gabatar da wani jawabi a madadin kasashe kusan 80 da suka hada da Brazil da Afirka ta Kudu, kan cika shekaru 30 da zartas da “Sanarwar Vienna da matakan da za a dauka” yayin taron hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD karo na 52, inda ya yi kira ga kasashen duniya da su kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu, tare kuma da sake tabbatar da ruhin sanarwar, ta yadda za a cimma burin samun ci gaba mai inganci.
Kasashen duniya suna kokari matuka domin neman samun dabarun kare hakkin dan Adam a cikin shekaru 30 da suka gabata karkashin gwarin gwiwar ruhin sanarwar, amma a sa’i daya kuma suna fuskantar kalubaloli da dama, kamar tsanantar nuna bambanci da rashin daidaito, da rarrabuwar kawuna da sauransu, duk wadannan sun kawo cikas ga aiwatar da sanarwar, da samun ci gaba mai dorewa.
A cikin jawabinsa, Chen Xu ya jaddada cewa, ya dace a dauki matakan da suka dace domin kawar da rashin daidaito yayin da ake kokarin kare hakkin dan Adam, kuma ya dace a mai da hankali kan batun ci gaba, musamman ma a kasashe masu tasowa, kana kamata ya yi kasashen duniya su gudanar da cudanya da hadin gwiwa a bangaren hakkin dan Adam bisa tushen daidaito da hadin kai da kuma martaba juna. (Mai fassarawa: Jamila)