Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya bayyana a yayin taron kwamitin sulhu na MDD cewa, kasar Sin tana kira da a hanzarta dawo da fitar da hatsi da takin zamani daga kasashen Rasha da Ukraine.
Geng ya kara da cewa, shirin samar da hatsi na tekun Bahar Aswad da yarjejeniyar fahimtar juna game da fitar da abinci da takin zamani na Tarayyar Rasha, na da matukar muhimmanci wajen kiyaye wadatar abinci a duniya baki daya, da ma daidaita kasuwannin abinci na duniya, don haka ya kamata a aiwatar da shi bisa tsari na daidaito, cikakke kuma mai inganci, haka kuma ya kamata a warware matsalolin bangarorin da abin ya shafa.
Kasar Sin na fatan bangarorin da abin ya shafa, za su yi aiki da hukumomin MDD, da karfafa tattaunawa da tuntubar juna, da martaba ka’idar moriyar juna, da kokarin warware matsalolin da suka shafi dukkan bangarori bisa daidaito, da hanzarta dawo da fitar da hatsi da taki daga kasashen Rasha da Ukraine, bisa la’akari da yanayin da ake ciki na kiyaye tsaron abinci a duniya, musamman ma bukatar kawar da matsalar abinci a kasashe masu tasowa.
Bayan da Moscow ta dakatar da shiga cikin yarjejeniyar fitar da hatsi a ranar 17 ga watan Yuli, ta kuma kai hari kan wuraren fitar da abinci na kasar Ukraine, lamarin da ya haifar da damuwa game da kokarin samar da abinci a fadin duniya. (Ibrahim)