Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya yi kira ga bangarori masu ruwa da tsaki da su samar da yanayin da ya dace na warware rikicin Ukraine baki daya.
Geng Shuang ya bayyana haka ne yayin wani taron kwamitin sulhu na MDD game da samar da makamai ga Ukraine.
A cewarsa, bisa la’akari da yanayin da ake ciki yanzu, duniya na bukatar dakatar da yaki maimakon samar da makamai, da tattaunawa maimakon ta’azzarar rikici, da kuma tattaunawar zaman lafiya maimakon fito na fito tsakanin kungiyoyin kasashe. (Mai fassarawa: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp