Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, ta ce matsayin Sin dangane da batun kamfanin TikTok a bayyane yake, kuma tana jaddada aniyar gwamnatin kasar na martaba hakkokin kamfanoni yadda ya makata.
Ma’aikatar ta ce Sin na maraba da matakin gudanar da shawarwari da kamfanoni bisa doron dokokin kasuwa, ta yadda za a iya kaiwa ga shawo kan matsaloli daidai da dokokin kasar Sin, da ka’idoji, da daidaita moriyar dukkanin sassa masu takaddama.
Ma’aikatar ta ce Sin na fatan Amurka za ta dauki makamancin wannan tafarki, ta cika alkawuran da ta dauka, da samar da wata kafa ta adalci, marar nuna wariya, kuma ta bunkasa muhallin kasuwanci ga kamfanonin kasar Sin, ciki har da kamfanin TikTok, ta yadda zai ci gaba da gudanar da hada-hada a Amurka, da ingiza daidaito, da ci gaba mai inganci, da dorewar alakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka. (Saminu Alhassan)