Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Dai Bing, ya yi kira ga kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ICC, da ta martaba ikon shari’a, da damuwar kasar Sudan yayin da ta ke nazartar batun yankin Darfur na kasar.
Dai Bing, wanda ya yi kiran a jiya Litinin yayin zaman kwamitin tsaron MDD game da ayyukan ICC, ya yi maraba da yadda mai gabatar da kara na ICC game da batun Sudan, ya ambato yadda gwamnatin Sudan din ke hadin gwiwa da kotun a fannin gabatar da kara, tare da bayar da Biza ga tawagar masu gabatar da kara ta kotun, da ma yadda kasar ta amince da wasu bukatun da za su tallafawa ayyukan kotun.
- Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam
- Xi Ya Nanata Bukatar Kare Al’adu Da Kayayyakin Gargajiya Na Sin
Dai ya jaddada cewa, har kullum kasar Sin na yayata bukatar warware batun yankin Darfur na Sudan ta hanyar siyasa, yana mai kira ga ICCn da ta lura da yanayi mai sarkakiya, da damuwar da ake nunawa game da batun Darfur yayin da take gudanar da ayyukan ta, musamman ga kasar ta Sudan da ma yankin da take.
Kaza lika, ya bukaci kotun da ta lura sosai da bukatun da aka sanya gaba, don gane da shawo kan rikicin kasar ta Sudan ta hanyar siyasa, da yin taka tsantsan, tare da kauracewa karya doka ta hanyar tsoma hannu cikin rikicin kasar. (Mai fassara: Saminu Alhassan)