Mataimakin zaunannen wakilin Sin a MDD, Geng Shuang, ya bayyana yayin bude zaman Kwamitin Sulhu na MDD game da rikicin Falasdinu da Isra’ila cewa, Sin na matsawa Isra’ila ta dakatar da ayyukan soja a zirin Gaza nan take, da dakatar da dukkanin ayyukan cin zarafin ikon mulkin kasa da tsaron Lebanon, da kuma daina danyen aikin dake barazanar jefa yankin cikin wani bala’i.
Geng Shuang ya bayyana cewa, taron musamman na gaggawa na MDD karo na 10 ya zartas da kudurin dake bukatar aiwatar da shawarwarin kotun kasa da kasa da Falasdinu ta gabatar a ranar 18 ga watan. Ya ce babban taron MDD yana bukatar Isra’ila ta daina mamaye kasa ba bisa doka ba, kuma yana matsawa bangarori daban daban da su daina samar da makamai ga Isra’ila don tallafa mata mamaye wata kasa daban. Ya nanata cewa, dole ne a tsaya tsayin daka kan dokokin kasa da kasa. Yana mai kira da a aiwatar da manufar kafa kasar Falasdinu mai ’yancin kai cikin sauri.
Geng Shuang ya kara da cewa, kudurin nan ya nuna matsayar da al’ummar kasa da kasa suka cimma wajen inganta warware matsalar Falasdinu, kuma ya nuna anniyar al’ummar kasa da kasa ta kiyaye adalci da cimma zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya. Ya ce bangaren Sin yana goyon bayan kwamitin sulhu na MDD da ya aiwatar da kudurin da abin ya shafa, da kuma gudanar da karin ayyuka don tsagaita bude wuta da saukaka bala’in jin kai, da kuma cimma zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya cikin sauri. (Safiyah Ma)