Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Fu Cong, ya ce Sin na kira ga Isra’ila da ta dakatar da aiwatar da matakan soji kan kasar Iran. Fu Cong, ya yi kiran ne a jiya Juma’a, bayan da Isra’ila ta kaddamar da jerin hare-hare ta sama kan sassa da dama a cikin kasar ta Iran, lamarin da ya sabbaba ruguza wasu cibiyoyin sarrafa nukiliyar kasar tare da hallaka mutane da dama.
Game da hakan, Fu ya shaidawa taron gaggawa na kwamitin tsaron MDD cewa, Sin na Allah wadai da matakin na Isra’ila, wanda ya yi matukar keta hurumin ‘yanci, da tsaro da ikon mulkin yankunan kasar Iran.
- Kula Da Kanki Bayan Haihuwa Abu Ne Muhimmi
- Sin Ta Bayyana Adawa Da Keta Hurumin ‘Yanci Tsaro Da Ikon Mulkin Yankunan Iran
Jami’in ya kara da cewa, Sin na adawa da kara ta’azzarar halin dar-dar da ake ciki, da bazuwar tashe-tashen hankula, kana tana matukar damuwa da sakamakon da aka iya biyo bayan hare-haren na Isra’ila.
Ya ce, Sin na nuna damuwa game da mummunan tasirin da halin da ake ciki ka iya yi ga tattaunawar nukiliyar Iran. A cewarsa, har kullum kasar Sin na mayar da hankali ga warware batun nukiliyar Iran ta hanyoyin tattaunawa da shawarwari, tana kuma adawa da nuna karfin tuwo, da kakaba takunkumai ba bisa ka’ida ba, da kaddamar da hare-hare kan cibiyoyin sarrafa nukiliya na ayyukan zaman lafiya.
Kazalika, wajibi ne a martaba hakkin kasar Iran na cin gajiyar makamashin nukiliya a ayyukan zaman lafiya, kamar yadda yarjejeniyar dakile bazuwar makamai ta kasa da kasa ta tanada. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp