Kasar Sin ta yi kira ga kasar Japan da ta yi karatun baya a tarihi, ta yi nazari mai zurfi kan abubuwan da suka gabata, ta kuma dauki bukatun kasar Sin da muhimmancin gaske, ta janye kalaman kuskure, tare da nuna halin dattaku na siyasa tsakaninta da Sin ta hanyar aiwatar da kwararan matakai.
Da yake bayyana hakan a yau Litinin, yayin taron manema labarai da aka saba gudanarwa, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian, ya ce dangane da batutuwa masu matukar muhimmanci, kamata ya yi bangaren Japan ya kawar da duk wata rufa-rufa ta kaucewa gaskiya. (Saminu Alhassan)
ADVERTISEMENT














