Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Dai Bing, ya yi kira ga kasashen duniya da su taimakawa kasar Somaliya wajen tunkarar kalubale daban-daban.
Dai Bing ya bayyana cewa, a yayin da tsarin siyasa da tsaro a kasar Somaliya ke cikin wani yanayi mai sarkakiya, bai kamata kasashen duniya su yi kasa a gwiwa ba, wajen nuna goyon bayansu kuma wajibi ne su taimakawa kasar Somaliya wajen tunkarar kalubale daga dukkan fannoni. .
Wakilin na Sin ya fadawa kwamitin sulhu cewa, ya kamata a yi duk mai yiwuwa, wajen ganin an karfafa nasarorin da aka cimma a yaki da ta’addanci. (Mai fassara: Ibrahim)