Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD Geng Shuang ya yi kira a jiya Talata ga kasashen duniya da su sauke nauyin dake wuyansu wajen daukar matakin fitar da makamai zuwa ketare, don tabbatar da tsarin hana fitar da makamai da kwamitin sulhu na majalisar ta gabatar, wanda ya tanadi cewa, kada a fitarwa wani yanki da ba kasa ba makamai, da yin takatsantsan wajen fitarwa yankunan dake fama da rikici makamai, da yin iyakacin kokarin hana makamai bazuwa cikin haramtacciyar hanya.
Kazalika, Geng Shuang ya yi jawabi a wata muhawarar da aka gudanar yayin taron tattaunawa kan manyan ka’idojin gudanarwa game da kananan makamai karo na 4 da majalisar ta gudanar, inda ya ce, cinikin irin wadannan makamai ba bisa doka ba na da alaka matuka da batun zaman lafiya da bunkasuwa, daya daga cikin muhimman batutuwan da a kan tattauna a bangaren kayyade makamai. Warware wannan matsala yadda ya kamata na da babbar ma’ana ga dakile ta’addanci da laifuffukan da ake aikatawa tsakanin kasa da kasa, da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyya-shiyya, da ma gaggauta bunkasuwar tattalin arziki da ci gaban al’umommin kasashen duniya.
Geng Shuang ya kara da cewa, gwamnatin Sin na mai da hankali matuka kan matsalar cinikin kananan makamai ba bisa doka ba, ko da yaushe tana matukar kayyade irin wannan makamai. Sin na fatan kara hadin gwiwa da sauran kasashe wajen taka rawar gani na raya wata duniya dake cike da zaman lafiya mai dorewa da tsaro da kawar da yin amfani da karfin bindiga, bisa tunanin kafa kyakkyawar makomar bil Adam ta bai daya da shawarwarin tabbatar da tsaron duniya, da na bunkasuwar duniya. (Amina Xu)