Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce bangaren Sin na fatan daukacin sassan masu ruwa da tsaki a jamhuriyar Nijar, za su hau teburin shawara domin warware sabani.
Yayin da take amsa tambaya game da halin da ake ciki yanzu haka a Nijar a Alhamis din nan, Mao Ning ta ce, “Muna zura ido kan abubuwan dake wakana a kasar, kuma mun saurari sanarwa daban daban da kungiyoyin AU da ECOWAS suka fitar.
A namu bangaren, Sin na kira ga sassan Nijar da su maida hankali ga kare moriyar kasa da al’ummar ta, kana su warware banbance-banbancen dake tsakanin su ta hanyar tattaunawa, da gaggauta maido da doka da oda, da kare yanayin zaman lafiya, da daidaito da ci gaban kasar.” (Saminu Alhassan)