Yayin da shugaba Bola Ahmad Tinubu ya tura sunan mutane 28 da za a nada a matsayin ministocin tarayyar Nijeriya kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, shiru ba a ga sunan wani daga Jihar Kano ya fito ba.
A yau, 27 ga watan Yuli, 2023, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya karanta jerin sunayen mutane 28 a gaban Majalisar.
- DSS Ta Gayyaci Tsohon Minista, Hadi Sirika
- Gwamna Uba Sani Ya Nada Bashir Zuntu A Matsayin Babban Akanta Na Jihar Kaduna
Sai dai a yayin da Shugaban Majalisar Dattawa ke karanto sunayen wadanda aka nada, har yanzu jerin sunayen ba su kare ba, lamarin da ke nuni da cewa Shugaba Tinubu zai tura karin sunayen.
Bangarorin siyasar Kano guda biyu wato Kwankwasiyya karkashin jagorancin Jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da kuma jam’iyyar APC karkashin jagorancin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, an dakatar da sunayensu sakamakon hatsaniya da ke ci gaba da kamari tsakanin bangarorin biyu.
Wata majiya ta shaida wa NIGERIAN TRACKER cewa dalilin rashin tantance sunayen ‘yan takara daga Kano shi ne yadda ‘yan jam’iyyar APC karkashin jagorancin tsohon Gwamna Ganduje ke matsawa shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu lamba kan kada ya nada Kwankwaso minista.
Majiyar ta bayyana cewa tsagin Gandujiyya sun dage cewa sun gwammace su rasa kujerar minista a maimakon su a bai wa babban abokin hamayyarsu, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, wanda ya jagoranci faduwar jam’iyyarsu a zaben 2023 a Kano.