Yau Alhamis, a gun taron manema labarai da kungiyar kasuwancin kasa da kasa ta Sin ta yi, kakakin kungiyar Sun Xiao ya mai da martani kan sakamakon da EU ta gabatar game da binciken da ta yi kan batun samun rangwame daga gwamnati dangane da motoci masu aiki da wutar lantarki kirar Sin.
Sun ya ce, tun bullowar wannan matsala, kungiyar kasuwancin kasa da kasa ta Sin ta dauki wannan batu da muhimmanci, tana goyon bayan Sin da Turai da su daidaita mabambantan ra’ayoyinsu bisa yin shawarwari, da ma kai ga matsaya daya wajen gabatar da wata manufa da ta dace dake biyan muradun bangarorin biyu da ka’idojin WTO. Sin na nacewa ga matsayin bin hanya iri daya da Turai da mai da hankali kan muradun dake jawo hankalinsu, da ma kin yarda da manufar ba da kariyar cinikayya, kana da ingiza bunkasuwar huldar ciniki tsakaninsu yadda ya kamata kuma mai dorewa, wanda zai zama ingantaccen abin dogaro ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya baki daya. (Amina Xu)