Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin yau Laraba, ta yi marhabin da “bayani mai kyau” da shugaban gwamnatin Jamus Plaf Scholz da sauran shugabannin kasashen Turai suka yi kan nuna rashin amincewa da yankurin ware kai ko mayar da wasu kasashe saniyar ware daga tsarin tattalin arzikin duniya.
A yayin taron kolin injiniya karo na 13 na kasar Jamus da ya gudana a Berlin jiya Talata, Scholz ya sake nanata muhimmancin dunkulewar duniya wajen samun ci gaba tare da nuna adawa da ra’ayin ware kai daga kasashe ciki har da kasar Sin. (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp