Hukumar dake lura da ayyukan binciken sarararin samaniya ta kasar Sin ko CNSA, ta bayyana a yau Juma’a cewa, an yi nasarar gwada ayyukan sadarwa da tauraron dan adam na Queqiao-2
CNSA ta ce tauraron dan adam na Queqiao-2 ya cika sharuddan aikin sa, zai kuma iya samar da tsarin sadarwa ga zango na 4 na aikin binciken duniyar wata, da ma wanda kasar ta Sin da sauran kasashe za su gudanar a nan gaba.
- Sin Na Goyon Bayan Yunkurin IAEA Na Tabbatar Da Tsaron Tashar Nukiliya Ta Zaporizhzhia
- Sin: An Fitar Da Tsarin Tallafin Kudade Domin Bunkasa Ci Gaba Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba
Kaza lika, a ranar 6 ga watan Afirilun nan, tauraron na Queqiao-2 ya kammala aikin sadarwa cikin nasara tare da kumbon Chang’e-4, wanda a yanzu ke gudanar da ayyukan bincike a sashe mafi nisa na duniyar wata. Har ila yau, tsakanin ranaikun 8 zuwa 9 ga watan na Afrilu, tauraron ya gudanar da ayyukan sadarwa na gwaji tare da na’urar bincike ta Chang’e-6, wadda kawo yanzu ba a kai ga harba ta samaniya ba.
Tun a ranar 20 ga watan Maris da ya shude ne aka harba tauraron dan adam na Queqiao-2, ya kuma shiga falakinsa a ranar 2 ga watan nan na Afirilu bayan gyaran da aka yi masa yana tsaka da tafiya, da rage saurinsa a kusa da doron wata, da kuma sarrafa shigarsa kewayen duniyar wata. (Saminu Alhassan)