A yayin taron BRF da aka kammala, babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya yi jawabi da ya ja hankalin mahalarta taron, wanda a cikin sa ya bayyana manufar “Gina hanyar siliki ba tare da gurbata muhalli ba”, a matsayin matakin warware kalubalen da ake fuskanta, tare da share fagen tunkarar sabuwar turbar da za ta amfani bil adama, da ma duniyar da yake rayuwa cikin ta.
Cikin shekaru 10 da suka gabata, an gina tashar samar da lantarki ta hasken rana a tuddan kudancin Amurka, an kuma samar da tashar lantarki ta iska, mafi girma a yankin tsakiyar Asiya a hamadar Gobi, yayin da aka gina tashoshin samar da lantarki ta ruwa a kogin kudancin Asiya.
- Sin Ta Yi Matukar Takaici Da Matakin Da Amurka Ta Dauka Na Dakatar Da Kudurin Jin Kai A Gaza
- Zaben 2023: Takaddamar Kashi 94 Cikin 100 Na Kujerun Da Aka Lashe Ta Dora Shakku Kan INEC
Wadannan ayyukan hadin gwiwa da aka gudanar, karkashin shawarar ziri daya da hanya daya, sun saukaka wahalhalun da ake fuskanta ta fuskar karancin makamashi, kana matakin ya bunkasa amfani da makamashi mai tsafta, tare da samar da goyon baya ga manufar zamanantar da ci gaba a kasashen da ayyukan suka gudana.
Har ila yau, a shekarun 10, Sin ta gina shawarar ziri daya da hanya daya, karkashin tsarin hadakar kasashe, don samar da ayyukan ci gaba ba tare da lalata muhalli ba har sama da 150, tare da sama da kasashe 40, kana ta gina tsarin ziri daya da hanya daya, na hadin kai da abokan hulda a kasashe 32. Bugu da kari, ta yi alkawarin ba za ta gina sabbin tashoshin samar da lantarki masu amfani da kwal a kasashen ketare ba, wanda hakan ya zama babbar gudummawa da Sin din ke bayarwa, wajen bunkasa raya tattalin arzikin duniya bisa tsari mai dorewa, tare da rage fitar da iskar carbon mai dumama yanayi.
Yayin taron na BRF da ya kammala, Sin ta sanar da aniyar gudanar da wasu ayyuka 8, domin goyon baya ga gina ziri daya da hanya daya mai inganci, wanda daya daga cikin su shi ne bunkasa ci gaba maras gurbata yanayi. A kuma mataki na gaba, Sin za ta zage damtse wajen ingiza ci gaba maras gurbata muhalli, da samar da ci gaba ta hanyoyin rage fitar da iskar carbon, tare da sauran kasashe da suka shiga shawarar ziri daya da hanya daya, ta yadda za a kai ga cimma nasarar sauya fasalin masana’antu zuwa marasa gurbata yanayi. (Saminu Alhassan)