Hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin, ta yi watsi da bangaren rahoton kwamitin SAGO, na masana kimiyya mai bayar da shawara game da asalin kwayar cutar da ta haddasa annobar COVID-19, wanda hukumar lafiya ta duniya WHO ta fitar.
Wata sanarwa da hukumar ta fitar a Litinin din nan, ta ce a ranar 27 ga watan Yunin nan, kwamitin SAGO, ya wallafa wani rahoto game da tushen kwayar cutar SARS-CoV-2, wadda ta haddasa barkewar annobar COVID-19.
Sanarwar ta ce, duk da yake bincike mai zaman kansa da kwamitin SAGO ya gudanar bai nuna wata sabuwar shaida game da asalin kwayar cutar ba, bai kuma bayyana wani abu da ya saba da sakamakon binciken hadin gwiwa tsakanin Sin da WHO na watan Maris din shekarar 2021 ba, a hannu guda, wasu kasashe da daidaikun mutane sun shigar da harkalla, da tasirinsu cikin rahoton, wanda daga karshe ya kunshi bayanai marasa tushe daga jita-jita, wadanda suka yi matukar suka ga nagartattun bayanan kimiyya dake cikin rahoton mai tushe da aka riga aka gabatar.
Kazalika, rahoton na SAGO ya kunshi wasu bukatu marasa tushe kan kasar Sin, kamar dai yadda sanarwar ta hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin ta bayyana. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp