A yayin taron manema labaru na yau da kullum da ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin ta shirya Alhamis din nan, mai magana da yawun ma’aikatar ya bayyana cewa, tun bayan aiwatar da dokar cinikayya ta yanar gizo ta jamhuriyar jama’ar kasar Sin a shekarar 2019, yanayin kasuwanci ta yanar gizo a kasar Sin ya ci gaba da inganta, kasuwancin yanar gizo ya zama muhimmin bangaren tattalin arziki na zamani dake da mafi girman ci gaba, mafi karade sassa, kuma mafi yawan kasuwancin da kirkire-kirkire.
A cewar ma’aikatar kasuwanci ta kasar Sin, kasar Sin ta zama kasuwa mafi girma a duniya wajen sayar da kayayyaki ta yanar gizo tsawon shekaru 11 a jere. A cikin shekaru biyar da suka gabata, yawan masu sana’ar kasuwanci ta yanar gizo a kasar Sin, ya karu daga miliyan 47 zuwa sama da miliyan 70.
Haka kuma, 13 daga cikin yarjejeniyoyin cinikayya cikin ‘yanci 22 da kasar Sin ta sanya hannu, sun hada da abubuwan da suka shafi cinikayya ta yanar gizo. An shigar da dokar kasuwanci bisa adalci ta yanar gizo ta kasar Sin, a cikin kundin bayanan manufofin jama’a na kasashen kungiyar APEC, wanda ya ba da gudummawar hikimar kasar Sin ga tsarin tafiyar da harkokin intanet na duniya. (Mai fassara: Ibrahim)