Kasar Sin ta bayyana matukar rashin gamsuwa da adawa da matakan kuntatawa da Amurka ta dauka bisa dogaro da abun da ta kira sakamakon bincike na sashe na 301, kan bangarorin da suka shafi harkokin Sin na teku da na jigila da ginin jiragen ruwa.
Ma’aikatar kasuwanci ta Sin ce ta bayyana hakan a yau Talata.
Da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida, kakakin ma’aikatar ya ce matakin na Amurka ya nuna yadda take yin gaban kanta wajen daukar matakai da nuna kariyar cinikayya, lamarin da ya keta dokokin hukumar kula da cinikayya ta duniya WTO da illata ka’idar daidaito da moriyar juna dake cikin yarjejeniyar sufuri cikin teku ta Sin da Amurka, haka kuma zai yi mummunar illa ga masana’antun Sin masu ruwa da tsaki a bangaren.
A ranar 10 ga wata ne kasar Sin ta sanar da cewa za ta sanya farashi na musammam na shiga tashoshin jiragen ruwa kan jiragen ruwa masu regista ta Amurka ko wadanda Amurka ta kera ko mallakinta ko kuma take da wani kaso na mallakarsa ko kuma yake karkashin wani kamfani ko hukumar Amurka.
Kakakin ya kara da cewa, matakan na Amurka ba tsaiko kadai za su kawo ga tsarin samar da kayayyaki a duniya ba, za su kara tsadar hada-hadar cinikayya ta kasa da kasa da kara farashin kayayyaki a cikin Amurkar da yin tsaiko ga takara da aikin yi a tashoshin ruwan Amurka da jefa juriya da amincin tsarinta na samar da kayayyaki cikin mawuyacin hali. (Fa’iza Mustapha)