A kwanakin baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ziyarci lardin Heilongjiang da ke arewa maso gabashin kasar Sin, domin yin ziyarar gani da ido, a yayin ziyarar, ya jagoranci wani taron karawa juna sani game da farfado da yankin arewa maso gabashin kasar Sin a sabon zamani, inda ya ba da shawarwari, da hanyoyin farfado da yankin arewa maso gabashin kasar Sin da makomar farfado da yankin a dukkan fannoni.
A halin yanzu, Sin tana kokarin sa kaimi ga farfado da al’ummar kasar Sin ta hanyar zamanintar da kasa bisa salon kasar Sin. Xi Jinping ya ba da shawarar cewa, don inganta zamanantarwa irin na kasar Sin, ya zama tilas a karfafa aikin taimakawa yankin arewa maso gabashin kasar Sin bisa manyan tsare-tsare. Xi ya bayyana cewa, tushen farfardo da yankin arewa maso gabashin kasar shi ne raya tattalin arzikin yankin, kana ya kamata a gudanar da kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha, da kuma kyautata sana’oi. Wannan ya shaida tunanin shugaba Xi Jinping a fannin raya tattalin arziki.
Shugaba Xi Jinping ya fi maida hankali ga yin kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha, ya jaddada cewa, ya kamata a yi amfani da kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha wajen bunkasa sana’oi, da kuma farfado da sanaoi a dukkan fannoni.
Kana a sa kaimi ga bunkasa sha’anin kerawa mai inganci, da kyautata sha’anin samar da kayayyaki. A yi amfani da albarkatun kirkire-kirkire a fannin kimiyya da fasaha don sa kaimi ga raya sabbin sana’oi bisa manyan tsare-tsare. (Zainab)