Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a gun taron manema labarun da aka gudanar a yau cewa, shirin raya duniya ya dace da tunanin bude kofa ga kasashen waje da amincewa da bambance-bambance, Sin tana maraba da dukan kasashe da kungiyoyin duniya da su shiga shirin da hadin gwiwar raya duniya.
Zhao Lijian ya yi bayani da cewa, a gun taron koli tsakanin shugabannin kasa da kasa kan batun ci gaban duniya da aka gudanar a kwanakin baya, shugabannin kasashe da dama sun nuna yabo ga wannan shiri, inda suka yi imanin cewa, shirin ya dace da bukatun ci gaban gaggawa na kasashe, musamman kasashe masu tasowa, wanda ya samar da wata hanya don gaggauta cimma burin samun bunkasuwa mai dorewa nan da shekarar 2030.
Zhao Lijian ya bayyana cewa, a mataki na gaba, Sin tana son yin hadin gwiwa da kasa da kasa don aiwatar da sakamakon da aka cimma a gun taron, da sa kaimi ga kasa da kasa da su mai da hankali ga batun samun bunkasuwa, da kara zuba jari a fannin samar da albarkatu a hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa, da yin kokari tare don inganta hadin gwiwarsu a fannonin yaki da talauci, da samar da isasshen abinci, da yaki da cutar COVID-19, da alluran rigakafin cutar, da tara kudade wajen raya kasa, da sauyin yanayi, da samun bunkasuwa ba tare da gurbata muhalli ba, da dai sauransu. (Zainab)