Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka Ned Price ya nuna cewa, Sin ba ta gabatar da bayanai na hakika dangane da COVID-19 a cikin kasar.
Game da hakan, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a gun taron manema labarai da aka yi a yau cewa, tun barkewar cutar, Sin ta rika musanyar bayanai da kasashen duniya cikin aminci.
Alkaluman kididdiga na nuna cewa, a cikin wadannan shekaru 3 da suka gabata, Sin ta yi mu’ammalar fasaha da WHO fiye da sau 60. Haka kuma Sin ta ci gaba da musanyar bayyanan kwayoyin cutar da masu kamuwa da cutar da kasashen duniya ta rumbun adana bayanan mura bisa sauyawar yanayi.
Gwamnatin Sin ta dauki matakan da suka dace don kare rayuka da lafiyar jama’arta da ma ingiza hadin kan kasa da kasa wajen magance cutar tare kuma da sa kaimi ga farfadowar tattalin arziki, Sin ta taka rawar a zo a gani. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp