An kammala taron kolin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka na Beijing. A yayin taron manema labarai na yau, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta yi martani kan yadda wasu kafofin yada labaru na kasashen yammacin duniya ke zuzuta batun bashin da ake bin kasashen Afirka, inda ta ce, tun bayan da aka kafa dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka shekaru 24 da suka gabata, dandalin ya taka muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga bunkasuwar kasashen Afirka, da inganta rayuwar jama’ar Afirka, wanda ke taimakawa Afirka warware sarkakiyar dake tattare da samun ci gaba da matsalar bashi. A yayin taron, shugabannin Afirka da dama ciki har shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramophosa, sun bayyana cewa, jarin da kasar Sin ke zubawa a Afirka, bisa hadin gwiwa ce ta moriyar juna, kuma ba zai jefa Afirka cikin “tarkon bashi” ba.
Mao Ning ta jaddada cewa, kasar Sin ba ta taba zama babbar mai baiwa Afirka rancen kudi ba. Bisa kididdigar da bankin duniya ya fitar, a cikin basussukan da ake bin kasashen Afirka, yawan basussukan da kasashen Afirka suka karba daga bangarori da dama da masu ba da lamuni da bashi masu zaman kansu ya kai kashi 80 cikin 100, yayin da basussukan da ke tsakanin bangarorin biyu ke daukar kaso mara yawa. Duk da haka, a ko da yaushe kasar Sin tana taimakawa Afirka wajen sassauta matsin lamba da yafe basussuka a tsakanin bangarori biyu da ma tsakanin bangarori daban-daban, kuma ita ce kasar da ta fi ba da gudummawa ga shirin yafe basussuka na G20. A cikin shirin aikin da aka amince da shi a wannan taro, kasar Sin ta kuma gabatar da shawarar wasu matakai na yafe basussuka.
Mao Ning ta kara da cewa muna kira ga kasashen duniya, musamman kasashen da suka ci gaba, da cibiyoyin hada-hadar kudi na kasa da kasa, da su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu, da taimakawa kasashen Afirka wajen sauke nauyin basussuka, da samun ci gaba mai dorewa. (Yahaya)