Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da gudanar da hadin gwiwa tsakaninta da kasa da kasa wajen samar da hidimar kiwon lafiya, domin taka rawa wajen inganta lafiyar al’ummomin duniya.
Rahotannin sun bayyana cewa, gwamnatin kasar Zambiya ta ba da lambar yabo ta “hadin gwiwar sada zumunta tsakanin kasa da kasa” ga tawagar sojoji masana kiwon lafiya da gwamnatin kasar Sin ta tura ga Zambiya a karo na 25, inda kasar ta bayyana godiya matuka ga kasar Sin bisa kokarinta na tura ingantattun masanan kiwon lafiya zuwa kasar, cikin dogon lokaci.
Game da wannan, Mao Ning ta bayyana a jiya cewa, sojoji masanan kiwon lafiya na kasar Sin, suna kokarin ceto rayukan majinyata a Zambiya, a sa’i daya kuma suna horas da likitocin sassan kasar bisa hakikanin yanayin da suke ciki, lamarin da zai kyautata tsarin kiwon lafiya a kasar. (Mai fassarawa: Jamila)