Game da bukatar da hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO ta gabatarwa kasar Sin, ta ba ta sahihan bayanai kan cutar COVID-19, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, tun bayan barkewar cutar COVID-19, Sin ta ci gaba da shaidawa duniya abubuwa da kididdiga game da cutar a fili, Sin ta ba da gudummawa ga kasa da kasa wajen yin nazarin allurar rigakafin cutar da maganin yaki da cutar. Sin ta kiyaye yin hadin gwiwa tare da hukumar WHO. Alkaluman kididdiga na nuna cewa, bayan da aka fara gano cutar, bangarorin biyu sun yi mu’amalar fasahohi sau a kalla 60 kan magance yaduwar cutar, da ba da jinya, da nazarin allurar rigakafin cutar, da gano asalin kwayar cutar da sauransu.
Mao Ning ta bayyana cewa, a halin yanzu, ana iya shawo kan cutar COVID-19 a kasar Sin. Bayan da aka kyautata matakan yaki da cutar a kasar, Sin za ta ci gaba da yin mu’amalar fasahohi tare da hukumar WHO. Kana Sin tana fatan sakatariyar hukumar WHO za ta tsaya tsayin daka kan matakai na kimiyya da daukar matakai masu dacewa cikin adalci, da yin kokarin samar da muhimmiyar gudummawa wajen tinkarar kalubalen cutar COVID-19 a duniya. (Zainab)