Wata sanarwa da hukumar kwastam ta Sin ta fitar, ta ce za a gudanar da sauye sauye a wasu bangarorin harajin hajojin da ake shige da ficen su a kasar Sin a shekara mai kamawa.
A cewar sanarwa, wadda aka fitar a Alhamis din nan, za a fara aiwatar da sauyin ne tun daga ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2024, kuma Sin za ta aiwatar da rangwamen haraji kan kayan da take shigowa da su har nau’o’i 1010.
- Firaministan Sin Ya Jaddada Bukatar Kyautata Yanayin Kasuwanci Da Kara Habaka Kasuwanni
- Sin Ta Kara Tallafin Kudi Don Maido Da Wuraren Kiyaye Ruwa A Yankunan Da Girgizar Kasar Ta Shafa
Sanarwar ta kara da cewa, domin ci gaba da bunkasa bude kofa mai inganci, bisa yarjejeniyoyin cinikayya maras shinge, da muhimman yarjejeniyoyin cinikayya da kasar ta sanya hannu tare da sassan kasashe ko yankuna, a shekarar ta 2024, za ta dora harajin da aka amincewa da wasu kasashe ko yankuna 30, bisa yarjejeniyoyi 20.
Har ila yau, domin tallafawa, da taimakawa kasashe mafiya raunin ci gaba, ta yadda za su ingiza ci gaban kan su, kasar Sin za ta ci gaba da aiwatar da harajin musamman ga hajojin su a shekarar ta badi, muddin sun kulla huldar diplomasiyya da kasar Sin tare da musayar takardun da ake bukata. (Mai fassara: Saminu Alhassan)