A yau Lahadi 23 ga wata ne ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin, ya shirya taron yayata manufofi, inda jami’in ma’aikatar kasuwancin kasar ya bayyana cewa, ma’aikatar kasuwancin kasar, da babban bankin kasar, da babbar hukumar kwastam ta kasar, da sauran hukumomin da abin ya shafa, sun gudanar da bincike a birane, da larduna da yawansu ya kai 18 a fadin kasar, kana sun gabatar da shawarwari game da yadda za a dauki matakai daban daban, na ingiza ci gaban cinikin waje a kasar.
Matakan da za a dauka sun hada da samar da damammakin ciniki, da maido da bukukuwan baje kolin kayayyaki a zahiri a cikin gidan kasar Sin, da hanzarta aikin samar da katin zirga-zirgar kasuwanci, tsakanin kasashen mambobin kungiyar APEC, da maido da zirga-zirgar jiragen sama tsakanin kasa da kasa yadda ya kamata. A sa’i daya kuma, za a samar da tallafi ga kamfanonin kera motoci, ta yadda za su kafa, da kuma kyautata tsarin sayar da motoci zuwa ga ketare.
Ban da haka kuma, za a kyautata hanyar gudanar da ciniki. Alal misali, za a fitar da dabarun tafiyar da harkokin kasuwanci tsakanin mazauna wurare na kan iyakokin kasa, kuma za a ba da jagoranci ga kamfanonin kasar, domin su kara fahimtar manufofin haraji, yayin da suke gudanar da kasuwanci tsakanin kasa da kasa ta yanar gizo. (Mai fassarawa: Jamila)