Kwararre a cibiyar binciken fasahohin samaniya ta kasar Sin ko CAST, Zhang Qiao, ya ce cikin shekaru masu zuwa, Sin za ta fadada girman tashar binciken samaniyar ta zuwa sassa 6, daga 3 da ake da su a yanzu.
Zhang, wanda ya bayyana hakan a ranar Laraba, yayin taro na 74, na rukunin masanan harkokin binciken samaniya na kasa da kasa ko IAC, wanda ya gudana a birnin Baku, fadar mulkin kasar Azerbaijan, ya ce tashar binciken samaniya ta Sin za ta taka rawar gani, a matsayin ta na “Zangon Samaniya”, kuma sansani mai kusa da duniyar bil adama.
- Wakilin Sin Ya Yi Karin Haske Kan Ra’ayi Da Matsayin Kasarsa Game Da Yanayin Tsaro Na Kasa Da Kasa Da Kwance Damarar Makaman Nukiliya
- Hadin Gwiwa Tsakanin Masana’antar Sarrafa Karfe Ta HBIS Da Ta Smederevo
Kaza lika, a cewar masanin, bayan fadada ta, nauyinta zai kai tan 180, kusan daidai da kaso 40 bisa dari, na nauyin tashar samaniya ta kasa da kasa, wadda ta shafe sama da shekaru 20 tana aiki, kana ake sa ran dakatar da amfani da ita bayan shekarar 2030, kamar dai yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya bayyana.
Zhang ya kara da cewa, tashar binciken samaniya ta Sin, za ta shafe shekaru sama da 15 tana aiki, ba shekaru 10 da a baya aka yi hasashe ba.
Ya ce a yanzu haka, tashar na da sassa 3, da suka kunshi babban sashen Tianhe, da kuma dakunan gwaje gwaje biyu, wato Wentian da Mengtian. (Saminu Alhassan)