Wani shirin aiki na tsawon shekaru uku da aka wallafa jiya Alhamis na nuna cewa, kasar Sin za ta gina wata babbar cibiyar tattara bayanai ta sabbin na’urori, yayin da kasar ke kokarin daidaita masana’antunta dake samar da abubuwan hada kayayyaki.
Bugu da kari, kasar za ta gina cibiyoyin bunkasa fasahohin zamani guda hudu da cibiyoyin kirkire-kirkire guda hudu don muhimman sassa na masana’antar samar da abubuwan hada kayayyaki, bisa tsarin, wanda sassan gwamnati 9 suka gabatar, ciki har da ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa, zai gudana ne daga shekarar 2024 zuwa shekarar 2026.
Wani jami’in ma’aikatar ya bayyana cewa, masana’antar dake samar da abubuwan hada kayayyakin masana’antu, tana taka muhimmiyar rawa wajen zamanintar da masana’antu, kuma ta kai kusan kashi 30 cikin 100 na adadin kayayyakin da manyan masana’antu na kasar Sin ke samarwa.(Ibrahim)