Kwamiti mai kula da ka’idojin kakaba harajin kwastam na kasar Sin ya ba da wata sanarwa a yau Talata cewa, Sin za ta kakaba karin harajin kwastam bisa izinin majalisar dokokin kasar na kashi 10% da na 15% kan wasu kayayyaki kirar Amurka da za a shigar da su kasar Sin daga ran 10 ga watan nan da muke ciki.
Sanarwar ta ce, gwamnatin Amurka ta sanar da karin harajin kwastam na kashi 10% kan kayayyakin da za a shigar da su daga Sin bisa hujjar maganin Fentanyl a jiya Litinin.
- Mai Magana Da Yawun NPC: Tattalin Arzikin Kasar Sin Na Da Juriya Da Ginshiki Mai Kwari
- Za A Sake Gurfanar da Blatter Da Platini Kan Zargin Cin Hanci
Matakin da ta dauka a kashin kanta ya illata tsarin cinikin duniya tsakanin mabambantan bangarori, kuma zai kara dora wahalhalu kan kamfanoni da masu sayayya na cikin gidanta, har ma da karya lagon tushen hadin gwiwar kasashen biyu na cinikayya.
Ban da wannan kuma, kakakin ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ya bayyana a yau Talata cewa, Sin ta riga ta kai kara a gaban hukumar cinikayya ta duniya WTO a bangaren daidaita bambancin ra’ayi. Kuma a wannan rana, ma’aikatar ta ba da sanarwar yanke shawarar shigar da sunayen kamfanonin Amurka 15, ciki har da Leidos cikin jerin sunayen kamfanonin da Sin ke kayyade shigo da kayayyakinsu kasarta.
Bayan hakan, Sin za ta ayyana kamfanin Illumina a matsayin kamfanin da ba a amince da shi ba a kasarta, kuma za ta hana shigo da na’urorinsa na nazarin kwayoyin hallita zuwa nan kasar Sin, sa’annan za ta sanya kamfanoni 10 ciki har da TCOM da sauransu a cikin jerin sunayen kamfanonin da ba su da aminci a kasarta. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp