A jiya Jumma’a ne hukumar sa ido kan harkokin bankuna da inshora ta kasar Sin, wato CBIRC, ta bayyana cewa, bankuna da kamfanonin inshora masu jarin waje, suna gudanar da harkokinsu lami lafiya a kasar Sin, kuma ta sake nanata alkawarin da kasar Sin ta yi, na kyautata muhalli, ga hukumomin hada-hadar kudi na kasashen ketare.
Alkaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa, ya zuwa karshen watan Satumban da ya gabata, bankuna masu jarin waje 202, na kasashe da yankuna 52, suna gudanar da harkokinsu a sassan kasar Sin. A cikinsu, bankunan da ‘yan asalin kasashen waje suka kafa a kasar Sin sun kai 41, kuma rassan da bankunan sauran kasashe, da yankunan Hong Kong, da Macao, da lardin Taiwan na kasar Sin suka kafa sun kai 117, kana ofisoshin bankunan da aka kafa a kasar Sin sun kai 131.
Gaba daya, bankuna masu jarin waje dake kasar Sin sun kai 895, wadanda kadarorinsu suka kai kudin Sin yuan triliyan 3.79, wato kwatankwacin dalar Amurka biliyan 520.
Ban da haka, adadin kamfanonin inshora masu jarin waje a kasar Sin ya kai 67, kana hukumomin inshorar kasashen waje 73, sun kafa ofisoshinsu a kasar Sin, inda gaba daya kadarorinsu suka kai kusan yuan tiriliyan 2.33. (Mai fassara: Jamila)