Gwamnan babban bankin kasar Sin Pan Gongsheng, ya ce kasar za ta samar da cibiyar kasa da kasa ta gudanar da hada-hadar kudin RMB na dijital.
Pan, wanda ya bayyana hakan a Larabar nan, yayin taron Lujiazui da ya gudana a birnin Shanghai na gabashin kasar Sin, ya ce makasudin kafa cibiyar shi ne bunkasa hada-hadar kudin RMB na dijital tsakanin sassan kasa da kasa, da ciyar da hidimomin raya kasuwannin hada-hadar kudade gaba, baya ga tallafawa kirkire-kirkire a fannin hada-hadar kudaden dijital. (Saminu Alhassan)













