Firaministan kasar Sin Li Qiang, ya ce kasar Sin a shirye take ta yi aiki wajen kare tsarin cinikayya tsakanin mabanbantan sassa bisa matukar himma, tare da kasancewa cikin shirin aiki tare da dukkanin sassa, don kare martabar cudanyar mabanbantan sassa bisa gaskiya.
Li, ya yi tsokacin ne cikin jawabinsa a yau Litinin, yayin taron shugabanni karo na biyar, na cikakkiyar yarjejeniyar kawance ta cinikayya cikin ‘yanci ta yankin Asiya da Fasifik ko RCEP, wanda aka bude a birnin Kuala Lumpur na kasar Malaysia.
Kazalika, a birnin na Kuala Lumpur, yayin da yake jawabi a dandalin taron kasashen gabashin Asiya karo na 20, Li Qiang ya ce Sin a shirye take ta yi aiki tare da mabanbantan sassa, wajen ingiza aiwatar da shawarar kyautata jagorancin duniya, da hada karfi-da-karfe wajen ingiza nasarar samar da zaman lafiya da ci gaban shiyyarta. (Mai fassara: Saminu Alhassan)














