Yayin wata hira ta musamman ta kafar bidiyo da ya yi da manema labarai, na kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin a baya-bayan nan, Sir Sherard Cowper-Coles, shugaban majalisar harkokin kasuwanci tsakanin Sin da Birtaniya, ya ce kasashen Birtaniya da Sin, za su ci gajiyar kud-da-kut a fannin zuba jari da huldar kasuwanci. Ya yi amfani da wani karin magana na Turancin Ingilishi, dake bayyana cewa, “Karuwar ruwa a teku na taimakawa tafiyar jirgin ruwa.”
Sherard Cowper-Coles ya ce “manyan jiragen ruwa biyu na Biritaniya da Sin, za su yi shawagi da kyau a ruwa mai karuwar wadata”.
A kwanan baya, Sherard Cowper-Coles, da sauran wakilan majalisar harkokin kasuwanci na Sin da Birtaniya sun ziyarci wasu biranen kasar Sin, ciki har da Shenzhen, da Shanghai, da Beijing da kuma Guangzhou. Bayan rangadin na su, Cowper-Coles ya bayyana cewa, ya gano cewa, kamfanonin Birtaniya dake kasar Sin, sun fi kyautata zaton samun bunkasuwar kasuwannin kasar Sin.
Ya ce, a shekarar 2022, yawan cinikayyar da ke tsakanin kasashen Birtaniya da Sin ya kai wani sabon matsayi, kuma dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu ta shiga wani sabon mataki. Cowper-Coles ya kara da cewa, sana’o’i da yawa na Birtaniya suna da damar samun ci gaba sosai a kasuwannin kasar Sin, kaza lika kayayyakin da suka hada da motoci, da tufafi, da kifin salmon, na samun karbuwa sosai ga masu sayayya na kasar Sin. A sa’i daya kuma, kasar Birtaniya ita ma na shigo da tarin kayayyaki daga kasar ta Sin.
Da yake magana kan fannonin zuba jari da ake da damar yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu, Cowper-Coles ya ce, kasashen Birtaniya da Sin sun dukufa, wajen cimma burin rage gurbata muhalli. Bugu da kari, karuwar bukatun kiwon lafiya na masayan kayan kasar Sin, na samar da damammaki ga kamfanonin Burtaniya a fannonin kiwon lafiya, da kimiyyar rayuwa da dai sauransu. Ya kuma yi maraba da yadda kasar Sin ke ci gaba da inganta bude kofa a fannin harkokin kudi. (Mai fassara: Bilkisu Xin)