Sani Shaaban, siriki ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, kuma tsohon dan takarar gwamna a jam’iyyar APC a Jihar Kaduna, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar mai mulki.
Tsohon dan majalisar wakilai, wanda ya tsaya takarar gwamna a watan Mayun 2022, ya bayyana haka a ranar Litinin, a wata wasika da ya aike wa shugaban jam’iyyar APC, Hanwa Ward a karamar hukumar Sabon Gari ta jihar.
- Matasan Sin Masu Fasaha Sun Lashe Lambobin Yabo Bakwai A Gasar Duniya
- Gwamnati Ta Dage Ranar Dawo Da Zirga-Zirgar Jirgin Kasan Kaduna Zuwa Abuja
A cewar Shaaban, jam’iyyar APC a Jihar Kaduna ba ta da wani abin da ya shafi rayuwar bil’adama, zamantakewa, da bin doka da oda, shi ya sa ya yanke shawarar barin jam’iyyar.
Sha’aban ya ce ba zai iya ci gaba da zama a jam’iyya mai mulki a halin da ake ciki a yanzu ba, inda a cewarsa, ba a la’akari da muradun mafi yawan jama’ar jam’iyyar a jihar.