Assalamu alaikum masu karatu barkammu da sake haduwa daku a wannan makon a cikin sabon shirin na mu mai suna ko kin san.
Uwargida ya kamata ki san kin hada duk wani abubuwa da da na miji yake bukata a wajen ‘ya mace.
- Ko Kin San Yin Tsarki Da Ruwan Sanyi Na Da Illa?
- Uwargidan Gwamna Ta Jagoranci Tattaki Kan Yaki Da Cutar Sikila A Jihar Zamfara
Kina da tsafta, kin iya daukan wanka, kin iya kwalliya, kin iya gyaran jikinki, gidanki kamshi, jikinki kamshi, ‘ya’yanki tsaf, kin iya daurin dankwali, kin iya tafiya, tafiyar da kike yi ma a gabansa daban take, ba fa wai tafiyar da za ki yi a kicin ba da tsakar gida da waje ba a’a, idan yana gida yana falo in kika doso shi tafiya za ki yi kina girgiza jikinki ko ina naki yana girgiza yana motsi kina karkada ko ina, ba wai tafiya za ki yi kamar an kado saniya ba, kina taku daidai kina dan kada kanki haka kina dan lunsa idanuwanki.
Amma sai ki ga duk irin wadannan abubuwa wai muna yi su ne kafin aure, mai makon lokaci da aka ce an daura auranki kin tare gidanki a lokacin ne ma ya kamata ki fid da sabbabin abubuwan jan hankali ga mijinki saboda a lokaci ne ya zama naki, a’a kuma shiken ke kin gama gyaran jikinki kwalliya babu dan turaren nan ma babu kina tafe na busa wari dan dauri dankwalin nan ma wata tamanta ma yadda ake yi sai de maigida ya kalla a waje, kida kaca-kaca to dan Allah gaya min ta yaya maigida ba zai yi sha’awar wata a waje ba? Mu muke tura mazajemmu suke sha’awar wasu mata a waje.
Amma idan kika hada duk abubuwa da da na miji yake bukata a wajan ‘ya mace kin gama mallake mijin ki, ba wata wadda za ta burge shi a waje domin ya san idan ya zo gida zai samu kamar haka koma abin da ya fi haka.