Duba da faruwar wasu abubuwa biyu da suka wakana a kwanan baya, sai hakan ke nuni da karuwar ruruwar siyasar wannan Kasa ta Najeriya.
Babu shakka, tamkar wata sunna ce da ake tsimaye a duk lokacin da wani babban Zabe na Kasa ke kara karatowa, sai an rika yin kwalli da wasu ababe na ban mamaki, wadanda idan ba a irin wannan lokaci ba, da wuya ne a ga suna afkuwa haka saken.
Wadancan abubuwa biyu da su ka faru su ne kamar haka:
- Murabus Da Kwamishinan Raya Birnin Lagos Da Ya Yi Daga Kujerarsa, sai kuma
- Korar Dantakarar Kujerar Kujerar Shugaban Kasa Karkashin Jam’iyyar ADC Da Aka Yi.
Murabus Daga Kujerar Kwamishinanci
Hakika cikin gudanar da mulki a Nijeriyar yau, ba safai ne ake ganin mukarraban gwamnati na sauka daga kan kujerun iko ba.
Faro tun daga matakin karamar hukuma ko jiha har zuwa ga matakin Kasa. Duba da yadda lamura na son zuciya da su ka yi wa sha’anin mulki kuri a yau, daga nan mutum zai gaggawar ankarewa da cewa, rashin yin murabus din, na iya faruwa saboda mabanbantan dalilai iri-iri na son zuciya musamman.
Murabus Din Kwamishina Dr Idris Salako
Dr Salako ne kwamishinan raya birnin Lagos da aka kururuta saukarsa bisa radin-kai a daukacin kafofin yada labarai na Kasa.
Mai yi wa, ko don masu mulki a Nijeriya ba su faye yin irin wannan kunar-bakin-wake daga kan kujerunsu na ofis, hakan ne ke da nasaba da fantsamar labarin nan da nan a cikin Kasa bakidaya.
Babban dalilin da ya kai ga yin murabus da kwamishina Salako ya yi, bai wuce yawan rugujewar benaye da ake ta kan samu a jihar ta Lagos babu kakkautawa daga lokaci zuwa lokaci. Ko ranar Lahadi ma an sami rushewar wani dogon bene mai hawa bakwai a Oniru da ke a jihar ta Lagos. Inda mutane biyu su ka rasu, wasu da yawa kuma a na ta neman tono su ne a ranar faruwar lamarin.
Cikin jihar dai ta Lagos, a Watan Nuwambar Shekarar 2021, an sami wani bene shi ma da ya rufta, nan take sama da rayuka arba’in (40) su ka salwanta. Bugu da kari, akwai inda Dr Salako ke yin nuni da cewa, akwai daga masu irin wadancan dogwayen benaye da ke da wata alaka da kud da kud da gwamnati, sai ka ga ko da an dakatar da su daga cigaba da gine-gimen nasu da ba ya kan-ka’ida, sai a ga sun cigaba abinsu. Ko cikin ginin da ya durkushe cikin `yan kwanakin nan, akwai wanda tuni an dakatar da shi cigaba da yin ginin nasa, amma ya cigaba. Zancen nan da ake, shi ma wancan mutumi, na daga wanda rushewar ginin ta lakume.
Murabus Abin-yabo
Ko ma dai menene dalilin saukar wancan kwamishina, babu shakka ya aikata wani abin a yaba masa. Shi ke jagorantar sha’anin fasalta cikin birnin na Lagos, to amma sai cin-rayuka gine-gine ke yi, to menene amfaninsa ke nan?.
Idan ma yana hanawa ne, amma ake bi ta sama aki hanuwa, to ai gara da ya yada kwallon mangwaro ya huta da kuda. Irin abinda da daman wasu kwalamammun da ke bisa kujerar mulki ba su iyawa.
Ina amfanin cigaba da zama bisa kujera da wasu gwamnoni cikin wannan Kasa ke yi, alhali abinda ya rataya a kansu na tsare rayukan jama’a ya gagare su gagara? Saboda ma wani karfin hali, gwamna ya gaza kare rayukan jama’ar jiha, kuma wai sai a ji ma ya nada kwamishinan tsaro na jiha!!!
Shi kuma kwamishinan tsaron, yana ji yana gani ana ta asarar rayuka a jihar, amma ya gaza yin koyi da Dr. Salako ya yi murabus daga kujerar.
Haka a can matakin Kasa, sai a wayigari a na ta kashe al’umar Kasa da sunan ta’addanci, amma kememe sai jagororin tsaron Kasar su gaza yin murabus irin na Dr Salako!!!
Kamata ya yi, duk kujerar da mutum ya tsinci kansa bisa, ta hanyar zabe ne ko nadi, muddin ya kasa barkata abinda Dokar Kasa ke bida daga gare shi, lalle ne sai ya gaggauta zama Salako na biyu, ma’ana yai yo kasa, don ba da dama ga wadanda za su iya. Ba mutum ya kankame kujerar mulki ba.
Korar Dantakarar Kujerar Shugaban Kasa Na Jam’iyyar ADC.
Ba abin mamaki ba ne dab da zabe ko bayan kammala zabe mutum ya ji a na tuhumar “ya`yan jam’iyya da batun yi wa jam’iyya zagon-kasa, wanda aka fi sani da antifati. Sai dai, irin wannan zargi, za a ga cewa, ba safai ne ake yi wa dantakara shi ba, an fi yin zargin ne ga “ya`yan jam’iyya irin jagororin wasu kwamitoci, ko shugabannin jam’iyya, masu mulkin da wa’adin mulkinsu ya kare. Haka suma “ya`yan jam’iyya na can kasa, akan zarge su da yin antifati ga jam’iyyun nasu.
Wani abin mamaki na jam’iyyar ADC, ta yi shelar dakatar da dantakarar kujerar shugaban Kasa na jam’iyyar ne kacokan, bisa zarginsa da yi wa jam’iyyar wata kitimirmira ta karkashin kasa.
Dakatar Da Dantakara Dumebi Kachikwu
Kwamitin koli na jam’iyyar ta ADC me ya zauna a satin da ya gabata, tare da shelanta dakatar da dantakararsu na shugaban Kasa, Dumebi Kachikwu daga takarar tasa. Akwai manyan zarge-zarge musamman guda biyu da su ke yi masa, game da dakatarwar da aka yi masa.
An ce a na zarginsa ne da fitar da wani faifan bidiiyo, inda ya yi wasu kalamai masu hadarin gaske ga dorewar hadin-kan jam’iyyar a matsayin abu guda. Sun ma kara da cewa, irin wadancan kalamai na Kachikwu, za su raunata nasarar da ake sa-rai ga sauran kujerun takara na jam’iyyar.
Zargi na biyu da ake yi masa, na da alaka da kin nuna wani takamaiman shiri da yake da shi a kasa game da shirye-shiryen kamfen ga jam’iyya.
Ko ma wane dalili ne ya sanya tunbuke Kachikwu, `yan jarida sun nemi jin ta-bakinsa lokacin da aka yi sanarwar tsige shin, amma tsit, bai ce komai ba. Sai dai a zahirance, da ma jam’iyyar na cikin rudu na shugabanci tun gabanin iza-keyar Kachikwu, inda shugabannin jam’iyyar na jihohi 27 a Nijeriya su ka ja tunga, tare da neman lalle ne shugaban jam’iyyar na Kasa, Mr Nwosu, sai ya yi murabus ko su kawar da shi.
Ke nan, ya yi kusa a gama faiyace hakikanin dalilin hankade Kachikwu daga kan kujerarsa ta takara. Ba abin mamaki ba ne a siyasa, ya kasance dalilin tsige shin da aka yi, ba shi ne gaskiyar lamarin ba.
Bugu da kari, cikin irin wannan dambarwa, laifi na iya tabbata akan kowane bangare. Babu shakka manyan jam’iyyu a Kasa, kan yi amfani da wasu `yan korensu wajen dakushe kaifin kananan jam’iyyu a Kasa. A wasu lokutan ma, manyan jam’iyyun, su ke kafa irin wadannan kananan jam’iyyu ta karkashin kasa, don yin amfani da su, kafin zabe da kuma bayan zabe.
Sannan, kananan jam’iyyun da ba manyan jam’iyyu ne su ka kafa su ba, sukan yi duk mai uiwa wajen cusa yaransu cikinsu. Ke nan, irin wannan dambarwa tattare da kananan jam’iyyu ma ba a ga komai ba.
Amma wasu dalilan rikici a cikin wadancan kananan jam’iyyu ba su ne aka lasafto ba. Domin kuwa, wasu na yin rikici ne wajen samun shugabanci ko wata daukaka cikin jam’iyyun.
A wasu lokuta ma, a kan samu rikici a tsakanin jam’iyyun, saboda dalili na mallake jam’iyyun ta-karfi, koko wajen sayar da jam’iyyun ga masu mulki, koko babbar jam’iyyar adawa. Duk inda aka je aka dawo dai, akasarin rikice-rikicen na son zuciya ne.