Barkanmu da sake saduwa a wannan fili,a wannan mako mun kawo ra’ayoyinku a kan yadda ‘yan siyasa ke amfani da kudi wajen jan hankalin talakawa masu jefa kuri’a.
Da kuma jan hankalin masu kada kuri’a domin ganin sun yi amfani da cancanta sun zabi mutanen da za su yi musu aiki ba tare da la’akari da masu basu kudi ba a zaben 2023.
Muhd Basheer Sa’ad
Ni bana ganin laifin ‘yan siyasa a wannan lamarin saboda mafiyawancin su kasuwanci suka dauki siyasar su. Saboda haka sun saka kudi sun sayi kuri’a dole ne suyi yadda suka ga dama da talakawa tunda sun sayi ‘yancin su ne da kudi.
Don haka dole masu kasa kuri’u su hankalta da karba kudi yayin zabe saboda idan har ka yarda ka amshi kudi kuma ka zabi mutum to shakka babu ka sayar da ‘yancin ka kuma babu yadda zakai dole sai abinda ka gani
Yusuf Muhammad Jalingo
Kowanne talaka yanzu abinda yake cewa “Allaah ya zaba mana shugaba nagari” sabida jiki magayi don kowa yaji ajikinsa.
Matsalar shi ne talauci ne aka sakawa mutane na dole shi ne su kuma masu neman mulki ido a rufe suke amafani da wannan daman sai mukuma talakawa muke karba amma badon anason hakan ba.
Muna amfani da wannan dama wajen yi wa al’umma tuni a kan kar asake zaben tumun dare don duk me yin zabe atunanin zai iya banbance abu mai kyau da maras kyau.
Allaah ya zaba mana shugabanni nigari. Amiin
Baban Khairat
A Ra’ayi na kamata ya yi mutane (ordinary masses) su yi hakuri da yanayin da aka samu kai su duba chanchantan dantakara da za su zaba, Abin ban haushinma shi ne wai bayan shekaru hudu lokacin zabe kaga, ana raba wa mutane abinda ko abinci na ranan ba zai isheka watakila ba laifin masu zaben ba ne halin talauci da tsadar rayuwa ne, Amma kuma bashi zai sa kasa yarda ‘yancin kaba, fatanmu dai shi ne Allah ya bamu sa ar shugabannin na gari,
Mahdee Bashir
Duk wanda ya karbi kudi a wajen ‘yan siyasa kuma ya zabe shi to ya tabbata ya sayar da ‘yancinsa da ta al’ummarsa, fakat!!!
Nuruddeen Muhammad Funtua
A gaskiya wannan ba abune mai kyau ba, muna kira ga ‘yan siyasarmu da su gyara idai har gyaran ake so ayi.
It’z Jameel Moh’d
Kawai Allah ya bamu shugaba nagari amma dai duk wanda ya cire kudi ya sayi delegate sannan ya sayi talakawa saboda su zabe shi, Wallahi inya ci zabe ba zai mana aiki ba, yakamata mu yi amfani da hankalin mu wajen zaben shugaba na gari
Yahaya Aliyu Sani
To mu dai munsan da cewa talaka baida wani katabus, Allah ya zaba mana mafi alheri
Nazifi Haruna Iliyasu
To idan bera da sata daddawa ma da wari, matsalar da aka samu shi ne har yanzu tallaka bai san kansa ba, da yasan kansa da an samu saukin al’amurra, to abinda nake gani Idan har dan siyasa zai baka dan abinda bai taka kara ya karya ba ka zabe shi tofa duk yadda ya yi dakai daidai ne domin kuwa ba don Allah ka zabe shi ba, kudi ya biya ka, to amma da yake mafi a’ala ga tallaka shi ne ya cire kwadayi ya zabi wanda ya chanchanta.
Widad Isma’il
Ai gani ga wanne ya ishi wane tsoron Allah, ai ko wannan jarrabawar wannan gwamnati ya kamata mutane su san su waye su kwadayi a lasa maka zuma a baki zakin sa na dan lokaci zai bace maka a baki amma abin da zai biyo baya da kanka zaka kai wa kanka hisabi ba sai an kai ga gaci ba.
Sulaiman Muhammad
Gaskiya har yandu talakawa masu jefa kuri’a kunnansu bai yi laushi ba, tun kafin ranar zabe an fara basu omo da indome
Adamu Yunusa Ibrahim
Fatan alheri.
Hussein B Gama
Yanzu kam lamarin sai dai mubi da innalillahi saboda komai ya lalace