Hedikwatar tsaro (DHQ) ta ce dakarunta da ta tura don tabbatar da tsaro na cikin gida a fadin Nijeriya sun kashe ‘yan ta’adda 28, sun kama ‘yan ta’adda da abokan huldarsu 114, wadanda ake zargin barayin danye man fetur ne wasu kuma masu garkuwa da mutane ne sannan ta kubutar da mutane 82 da aka yi garkuwa da su.
Daraktan yada labarai na rundunar, Manjo Janar Edward Buba, wanda ya bayyana hakan a taronta na mako biyu-biyu kan ayyukan rundunar sojin Nijeriya a ranar Alhamis, ya ce sojojin sun kwace danyen mai da darajarsa ta kai Naira Miliyan N876,451,000.00.
Ya ce sojojin sun rufe ramukan satar man 36, kwale-kwale na katako 62, tankunan ajiya 73, mota daya, da Tukwanen girki 75 da barayin danyen man ke amfani da su.
Ya kuma tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa, jami’an rundunar sojin kasar za su ci gaba da bayar da tsaro kuma za su yi amfani da karfin soji kan duk wata kungiyar da ke barazana ga lafiyar ‘yan kasa da jami’an tsaro.