Rundunar Sojin Nijeriyta ta musanta zargin cin zarafin matan da suka tsira daga hannun boko haram a yankin arewa maso gabas.
Daraktan yada labarai na shalkwatar tsaron Nijeriya, Manjo Janar Edward Buba wanda ya mayar da martini game da zargin da Kungiyar Kare Hakkin Dan’adam ta Amnesty ta yi, ya ce dakarun Nijeriya suna aiki ne bisa kwarewa daidai da yadda doka ta tsara kuma ba tare da take hakkin bil’adama ba.
- Mayaƙan ISWAP Da Boko Haram 4 Sun Tuba Sun Miƙa Wuya A Borno
- Gwamnatin Kano Ta Bude Makarantun Da Ganduje Ya Rufe
Ya yi kira ga kungiyoyin kare hakkin Dan’adam su rika tuntubar rundunarsu da zarar sun ji wani abu domin tantance gaskiya kafin su kai ga yada wa duniya, domin hakan shi ne adalci.
A wani sabon rahoto da ta fitar, Kungiyar Kare Hakkin Bil’adama ta Amnesty International ta bayyana cewa an tsare mata da ‘yan mata ba bisa ka’ida ba an kuma ci zarafinsu a cibiyoyin tsare mutane na sojojin Nijeriya bayan da suka tsere daga hannun mayakan Boko Haram.
Rahoton ya ce an tsare wasu daga cikin matan tare da ‘ya’yansu tsawon shekaru saboda kawai zargin suna da alaka da kungiyar masu tsattsauran ra’ayin. Kungiyar Amnesty ta ambaci hirarraki 126, galibi da wadanda suka tsira daga wannan mummunan yanayin, a cikin shekaru 14 da masu tsattsauran ra’ayin addinin Islaman suka kwashe suna kaddamar da hare-hare.
Rahoton ya sake bayyana damauwa akan keta hakkokin bil’adama da aka zargi sojojin Nijeriya da yi, wadanda a baya aka zarge su da aikata hukuncin kisa na wuce gona da iri da kuma yin kame ba bisa ka’ida ba, a daya daga cikin rikice-rikice mafi dadewa da aka gani a duniya.
Ko da yake, rahoton ya lura cewa dabi’ar tsare mutane ba bisa ka’ida ba na tsawon lokaci bai bazu ba a cikin ‘yan shekarun nan.
Rundunar sojan Nijeriya ta yi watsi da rahoton a matsayin “mara tushe” kuma ta nanata cewa ta samu ci gaba wajen inganta kare hakkokin bil’adama kuma tana hukunta jami’anta da suka yi ba daidai ba.
Amma yanayin da wasu matan suka tsinci kansu a ciki bayan da suka tsere daga hannun ‘yan Boko Haram na da matukar muni, lamarin da ya sa wasunsu suka gwammace su koma wa ‘yan Boko Haram, abin da Niki Frederiek, mai bincike kan rikice-rikice na kungiyar Amnesty International, ya fada kenan game da cibiyoyin da ake tsare mutane a sansanonin soja da ke Jihar Borno.
Rahoton ya ce akalla mutum 31 da suka tsira da aka yi hira da su sun ce an tsare su ba bisa ka’ida ba a cibiyoyin, abin da ke nuna cewa wannan dabi’ar ta bazu.
“Dole ne hukumomin Nijeriya su tallafa wa wadannan ‘yan mata da mata yayin da suka koma cikin al’umma,” in ji Samira Daoud, Daraktar Kungiyar Amnesty International a Yammaci da Tsakiyar Afirka.