Rundunar sojin Nijeriya ta ce wasu sojojinta da ke yin sintiri a Jihar Borno sun yi hatsari.
Wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Alhamis, ta ambato rundunar soji na cewa “dakarun rundunar Operation Hadin Kai sun yi hatsari a yayin da suke sintiri a Arewacin Borno.
Runduna ta 3 da rundunar MNJTF sun tabbatar da cewa a cikin sojoji 30 da suka gamu da hatsarin babu wanda ya mutu.”
Sanarwar ta kara da cewa yanzu haka sojoji bakwai da suka jikkata suna samun kulawa a asibitin 7 Div. da ke Maiduguri.
Kakakin runduna ta 3 Operation Hadin Kai kuma kyaftin na Multinational Joint Task Force, Babatunde Zubairu, ya tabbatar da aukuwar hatsarin a Gajiram wanda ya rutsa da motar daukar kaya da ke dauke da sojoji kusan 30 da ke sintiri tsakanin Baga a arewacin Borno.