Sojojin Nijeriya sun kashe ƴan ta’adda takwas tare da daƙile yunƙurin yin garkuwa da wasu mutane 28 a jihohin Zamfara, Imo, Borno, da Sokoto a jiya Juma’a.
A Zamfara, Sojojin sun amsa kiran gaggawa a gundumar Ƴar Sabiya Wuya, inda suka yi artabu da ƴan ta’adda tare da ceto mutane 27 da aka yi garkuwa da su. An kai mutum ɗaya da ya samu raunin harbin bindiga zuwa wani wurin jinya.
- Sojoji Sun Kashe Boko Haram 4 A Borno
- EFCC Ta Miƙa Wa FBI $22,000 Da Ta Ƙwato Daga Hannun Masu Satar Kuɗaɗe Ta Yanar Gizo
Bayan samun sahihin bayanan sirri Sojojin sun cigaba da gudanar da sumame a ƙauyukan Gurusu da Kisema da Gana na Zamfara in da suka kashe ƴan ta’adda biyu tare da kwato baburansu.
A jihar Imo kuma Sojojin sun daƙile wani yunƙurin yin garkuwa da Yarima Chinonso Meremikwu a Umuaka, inda suka kashe ɗan ta’adda daya tare da kwato bindiga ƙirar AK-47, mujallu, da babur.
A jihar Borno, Sojojin sun kashe wani ɗan ta’adda guda a ƙauyen Forfor, inda suka kwace bindiga ƙirar kirar AK-47 da harsashi, tare da kashe wasu ƴan ta’adda biyu a Tuga, tare da kwato karin makamai da Kekunan hawa.
A jihar Sokoto kuwa Sojoji da jami’an DSS ne suka amsa kiran gaggawa don kai ɗauki lokacin yunƙurin garkuwa da mutane a hanyar kwanar Isa – Shinkafi, inda suka kashe ƴan ta’adda biyu ragowar suka tsere.