Rundunar sojin Nijeriya ta tabbatar da cafke daya daga cikin jami’anta, Lance Kofur Ahmed Aminu, dangane da mutuwar wani mai gyaran waya, Alkasim Ibrahim, a Karamar Hukumar Mayo Belwa ta Jihar Adamawa.
Lamarin da ya faru a ranar Juma’a ya jawo hankulan jama’a da kuma neman a yi masa hukunci.
- Rashin Ganin Shugabannin APC Yayin Ziyarar Shettima A Kano Ya Haifar Da Zazzafar Muhawara
- An Fitar Da Sanarwar Beijing Bayan Taron Ministocin Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Wayewar Kan Bil Adama
Wata sanarwa da mukaddashin Daraktan hulda da jama’a na rundunar soji ta 23 da ke Yola, Laftanar Adebayo Adewumi, ya fitar a ranar Asabar, ta bayyana cewa an kai sojan gidan kaso kuma ana ci gaba da gudanar da cikakken bincike kan lamarin.
“Rundunar sojin Nijeriya ta tabbatar da faruwar lamarin cikin matukar damuwa tare da fatan sanar da jama’a cewa an kama sojan da aka ce tuni yana gidan yari.
Sanarwar ta kara da cewa “An fara gudanar da cikakken bincike don tabbatar da al’amuran da ke tattare da lamarin,” in ji sanarwar.
Kakakin Brigade ya bayyana cewa ba za a yi kasa a gwiwa ba wajen magance duk wani yunkuri na sojojin Nijeriya wajen aikata aikin da bai dace ba, tare da tabbatar da da’a, da bin doka da oda.
Ya yi nuni da cewa ba za a iya jure duk wani nau’i na rashin da’a a tsakanin ma’aikatanta ba.
Ya kuma ba jama’a tabbacin cewa sakamakon binciken zai fito fili domin tabbatar da gaskiya da rikon amana da kuma adalci.
Rundunar ta kuma bukaci ‘yan kasar da su kwantar da hankalinsu, su guji yada jita-jita, ko kuma shiga ayyukan da za su kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a, tare da yin alkawarin tabbatar da martabarta da kuma bautar kasa.
A halin da ake ciki dai, kisan ya janyo cece-ku-ce a tsakanin mazauna yankin da kuma kungiyoyin kare hakkin bil’Adama, wadanda ke kira da a gudanar da bincike na gaskiya ba tare da nuna son kai ba kan lamarin da ya kai ga mutuwarsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp