Dakarun rundunar hadin gwiwa ta Operation Hadarin Daji (OPHD) sun ceto mutane 10 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a garin Tsafe da ke Karamar Hukumar Tsafe a Jihar Zamfara.
Wannan na cikin wata sanarwa da jami’in yada labaran rundunar, Laftanar Suleiman Omale ya fitar.
- Fasinjoji 15 Sun Bace Yayin Da Mahara Suka Farmaki Mota A Taraba
- Juyin Mulki: Sojojin Nijar Sun Fara Shirin Sakin Shugaba Bazoum
Ya bayyana cewa a daren ranar Talata 12 ga watan Maris, 2024 sojoji suka yi artabu da ‘yan bindiga a garin Tsafe.
Laftanar Omale ya bayyana cewa, “Ta hanyar tsauraran matakai da jajircewa, sojojin sun yi galaba a kan ‘yan bindigar, inda suka sa suka tsere da raunukan harbin bindiga, inda suka bar wasu mutane 10 da suka yi garkuwa da su.
Ya kuma yi karin haske kan sakamakon harin, inda ya ce a lokacin samamen sojojin sun yi nasarar kubutar da dukkanin mutanen 10 tare da mika su ga iyalansu.
Omale ya kara da cewa, “Kwarai sojojin sun nuna kwazo, jarumta, kwarewa wajen gudanar da aikinsu.”
GOC, Manjo Janar Mutkut ya bayyana jin dadinsa da irin kokarin da sojojin ke yi, ya kuma bukace su da su ci gaba da gudanar da ayyukansu na tabbatar da tsaro a fadin jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp