Dakarun Sojin Nijeriya sun ceto mutane 21 da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Mariga da ke Jihar Neja.
An ceto mutanen ne a ranar 9 ga watan Nuwamba, bayan dakarun sojin sun kai samame ƙauyukan Abaha da Sabon Wuri sakamakon bayanan sirri kan ayyukan ’yan ta’adda.
Rundunar sojin ta ce dakarunta sun yi musayar wuta da waɗanda ake zargi da ta’addanci, lamarin da ya tilasta musu tserewa zuwa wani daji, wasu kuma suka samu raunukan harbin bindiga.
Dukkanin mutanen 21 da aka ceto ba su samu rauni ba.
An ba su agajin farko kafin miƙa su ga hukumomin da abin ya shafa domin haɗa su da iyalansu.
Rundunar sojin ta ce tana ci gaba da sintiri domin kamo waɗanda suka tsere.
Ta kuma buƙaci mazauna yankin su kai rahoton duk wanda suka gani da raunin harbin bindiga ga jami’an tsaro.













