Sojojin rundunar Operation FANSAR YANMA sun ceto mutane 50 da ’yan bindiga suka sace tare da ƙwato shanu 32 da aka sace a ƙauyen Raudama, da ke ƙaramar hukumar Faskari ta Jihar Katsina.
An sace mutanen ne a ranar Lahadi, 27 ga watan Afrilu, 2025, lokacin da ’yan bindiga suka kai farmaki ƙauyen sannan suka kuma tafi da shanun.
- Shin Amurka Na Iya Komawa Kan Kadaminta A Matsayin Cibiyar Masana’antun Duniya?
- Akwai Ƙarin Gishiri A Yawan Masu Sauyin Jam’iyya Zuwa APC – El-Rufai
Majiyoyi sun shaida wa ƙwararren masanin tsaro na Maiduguri, Zagazola Makama, cewa harin ya faru da misalin ƙarfe 8 na dare.
Bayan harin, sojoji da ’yansanda sun hanzarta haɗa runduna ta musamman da ta bi sahun ’yan bindigar, inda suka fafata da su a wani gagarumin artabu.
Daga bisani dakarun suka samu nasarar fatattakar ’yan bindigar, sannan suka ceto mutanen da aka sace, tare da ƙwato shanun da suka sace.














